Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-22 10:59:53    
Kasar Iran za ta ba da amsa ga sabon shirin da kasashe 6 suka gabatar

cri

A ran 21 ga wata a gun wasu tarukan jama'a, shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa, kafin ranar 22 ga watan Agusta, kasar Iran za ta ba da amsa ga sabon shirin da kasashe 6 suka gabatar domin warware matsalar nukiliya ta kasar Iran.

A ran nan, shugaban kasar Amurka Bush wanda yake halartar taron koli na Turai da Amurka a birnin Vienna ya bayyana wa manema labaru cewa, lokacin da Mr Ahmadinejad ya diba ya yi tsawo sosai, yana fata kasar Iran za ta ba da amsa cikin makonni amma ba watanni da dama ba.

Firayin ministan kasar Austria wadda ke rike da shugabancin EU a wannan karo Wolfgang Schuessel ya ce, kada kasar Iran ta jinkirta lokacin ba da amsa cikin dogon lokaci, sabo da yanzu ya zama damar da ta fi kyau domin kasar Iran ta karbi wannan shiri da sake yin shawarwari da sauran kasashe.(Danladi)