A ran 20 ga wata a birnin Baku, babban birnin kasar Azerbaijan, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya bayyana cewa, kafin kasar Iran ta ba da amsa ga sabon shirin da kasashe 6 suka yi wato Amurka da Rasha da Sin da Britaniya da Faransa da Jamus, kasar Iran tana shirin yin shawarwari da kasashen duniya a kan matsalar nukiliyarta ba tare da sharadi ba.
A ran nan a birnin Moscow, shugaban kasar Rasha Putin ya yi imani cewa, za a iya janye takardar matsalar nukiliya ta Iran daga kwamitin sulhu na MDD, haka kuma za a iya sake mayar da ita zuwa hukumar makamashin nukiliya ta duniya.
A ran nan a birnin Washington , mataimakin kakakin majalisar ta kasar Amurka Adam Ereli ya ce, a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran, kasashen Amurka da Italiya suna da ra'ayi daya, kuma suna goyon baya ga sabo shiri da kasashe 6 suka yi.(Danladi)
|