Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 21:22:46    
Kasar Rasha ta sake nanata cewa, ba ta goyon bayan warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta karfin makamai

cri
Ran 20 ga wata a birnin Baku, babban birnin kasar Azerbaydzhan, Andrei Denisov, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasar Rasha ba za ta goyi bayon warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta karfin makamai ba a ko wani irin hali. Ran 19 ga wata, shugaba Bush na kasar Amurka ya karfafa yin kira ga kasar Iran da ta daina dukan ayyuka dangane da uranium masu inganci. Mahmou Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya jadadda cewa, kasar Iran ba za ta yi ko wane shawarwari game da matsalar nukiliya tare da sharadi ba.

Mr. Denisov ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi jawabi a taro na karo na 33 na majalisar ministocin harkokin waje na kungiyar musulunci. Ya ce, ba kwai za a warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta karfin makamai ba, har ma za a tayar da rikici mai tsanani, kasar Rasha tana ganin cewa, manufar warware rikici da kau da bambanci ta hanyar harkokin waje, wannan ita ce hanyar da ta fi kyau da ake zaba. (Bilkisu)