Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 19 ga watan nan a birnin Tehran , Mahmoud Ahmadi Nejad , Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa , ba zai karbi shawarwarin nukiliya tare da 'karin sharadi ba . A wannan rana shugaba Bush na kasar Amurka ya sake neman kasar Iran da ta daina aikace-aikacen ingancin uranium.
Gidan talabijin na kasar Iran ya watsa labari cewa , Mr. Nejad ya yi wannan bayani ne yayin da yake ganawa da Ayatollah Khamenei , shugaban koli na kasar Iran . Sa'an nan kuma ya nuna yabo ga sabon shirin da kasashe 6 suka gabatar don warware matsalar nukiliyar Iran . Ya ce , wannan mataki mai yakini ne da kasashen duniya suka gabatar . (Ado)
|