Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-19 17:57:23    
Shugaban kasar Ghana ya yi shawarwari da firayin ministan kasar Sin

cri

A ran 18 ga wata, shugaba John Agyekum Kufuor na kasar Ghana ya yi shawarwari da Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Ghana, inda suka yi musayar ra'ayoyinsu kan yadda za a kara yin hadin guiwa a tsakanin kasar Ghana da kasar Sin.

A gun shawarwarin, Mr. Kufuor ya ce, a ganin kasar Ghana, kasar Sin muhimmiyar abokiya ce wajen yin hadin guiwa. Bangaren Ghana yana son yin hadin guiwa tare da bangaren kasar Sin wajen sana'ar saka da ayyukan ban ruwa da aikin gona da aikin kamun kifi da sana'o'in zirga-zirga da yin sufuri kuma da sana'ar sadarwa. Mr. Kufuor yana fatan masana'antun kasar Sin za su iya kara zuba jari a kasar Ghana, kuma za su iya yin hadin guiwa da takwarorinsu na Ghana.

Lokacin da yake yin jawabi, Mr. Wen ya yaba wa gwamnatin Ghana sosai domin tana nuna goyon baya sosai ga kasar Sin wajen bin manufar Sin daya tak. Ya kara da cewa, bangaren kasar Sin yana son yin kokari tare da bangaren kasar Ghana kan yadda za a raya dangantakar hadin guiwa irin ta moriyar juna da amincewa da juna daga duk fannoni a tsakaninsu. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa kasashen Afirka taimako bisa karfinta. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsai da kudurin cewa za ta ci gaba da tura likitoci zuwa kasar Ghana, kuma za ta samar da maganin zazzabin cizon sauro da gina cibiyar yin yaki da zazzabin cizon sauro da gina wasu makarantun firamare a kauyukan kasar Ghana. Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta horar da wasu kwararrun da kasar Ghana take bukata.

Bayan da aka kawo karshen shawarwarin, Mr. Kufuor da Mr. Wen sun halarci bikin rattaba hannu kan "Yarjejeniyar yin hadin guiwa kan tattalin arziki da fasahohi a tsakanin gwamnatocin Ghana da Sin" da sauran yarjejeniyoyin da abin ya shafa. Daga karshe dai, bangarorin biyu sun bayar da wata Hadaddiyar Sanarwa. (Sanusi Chen)