Ziyarar da firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ke yi a kasashe 7 na Afirka ta jawo hankulan kungiyoyin tattalin arziki na jama'a da rukunin masana'antu na kasashen Sin da Afirka sosai, suna ganin cewa, ziyarar Mr. Wen za ta bude sabuwar kofar zuba jari da kugniyoyin jama'a na kasashen Sin da Afirka suke yi.
Lokacin yake zantawa da manema labaru a ran 19 ga wata, shugaban sashen yin cudanya na hadadiyyar kungiyar kasuwanci ta jama'a ta kasashen Sin da Afirka Mr. Chu Shuntang ya bayyana cewa, kungiyar wakilai ta kasar Sin da ke karkashin jagorancin Mr. Wen a wannan gami tana kunshe da wakilan rukunin masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin, haka kuma, a cikin kasashe 7 na Afirka da Mr. Wen zai kai musu ziyara akwai masana'antu masu zaman kansu na kasar Sin masu yawa, tabbas ne ziyarar da za a yi a wannan gami za ta ingiza yin mu'amalar tattalin arziki a tsakanin kungiyoyin jama'a na kasashen Sin da Afirka, ta yadda kungiyoyin jama'a na kasar Sin za su kara zuba jari a kasashen Afirka.(Tasallah)
|