Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 19:43:24    
Iran za ta mayar da martani a bayyane kan shirin kasashe shida a cewar ministan harkokin waje na kasar

cri

Jiya, a Tehren, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya furta, cewa Iran za ta mayar da martani a bayyane kan sabon shirin da kasashe shida suka fito da shi game da yadda za a daidaita maganar nukiliyar kasar.

Sa'annan Mottaki ya ce, kasar Iran za ta yi haka ne kamar yadda ta yi bayani ba tare da yin rufa-rufa ba kan yadda take yin harkokin inganta sinadarin Uranium. Ya kuma kara da ,cewa mahukuntan gwamnatin Iran sun yi hasashen, cewa wannan sabon shiri wani mataki ne mai yakini da aka dauka kan hanyar daidaita maganar nukiliyar Iran saboda yana la'akari da matsayin da bangarorin biyu suka dauka, amma duk da haka, gwamnatin Iran za ta yi nazari a kai cikin tsanaki kafin ta fito da shawararta ta kanta. ( Sani Wang )