Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-12 20:19:26    
Kasar Sin tana yin jarrabawar HSK

cri

Za mu gabatar muku da wata jarrabawar musamman da kasar Sin take shiryawa don mutanen kasashen waje da harshe na farko ba Sinnanci ba ne wato jarrabawar HSK. Jarrabawar HSK jarrabawa ce da gwamnatin kasar Sin take shiryawa don jarraba Sinnanci da mutanen kasashen waje suke iyawa, wadanda harshen uwarsu ba Sinnanci ba, kamar jarrabawar TOEFL da GRE da kasar Amurka take yi. An kafa azuzuwa guda 11 bisa makin da aka samu, a cikinsu kuma aji na 11 aji ne na koli.

Wang Lujiang, shehun malama ta jami'ar koyon harsuna ta Beijing, ta dade tana sa hannu cikin ayyukan da suka shafi jarrabawar HSK. Ta waiwaya inda ta ce, kasar Sin ta fara shirya jarrabawar HSK tun daga shekarar 1990, a lokacin nan mutane fiye da dubu 2 sun shiga wannan jarrabawar da aka yi a karo na farko. Amma ko kusa halin da ake ci a yanzu bai yi daidai da na da ba. Ta ce,

'a cikin shekaru 1990, a galibi dai masu shiga jarrabawar HSK dalibai ne da ke koyon Sinnanci a jami'o'i na kasar Sin da na kasashen waje, bayan shekarar 2000, ban da dalibai kuma, 'yan makarantar firamare da midil da ke koyon Sinnanci su ma sun shiga wannan jarrabawa, mutanen da suke koyon Sinnanci da kansu sun shiga jarrabawar don jarraba sakamakon da suka samu. Har zuwa shekarar 2005 da ta gabata, jimlar mutanen da suka shiga jarrabawar HSK ta kai dubu dari 5 gaba daya. '

An ce, bayan da suka sami takardun shaidar matsayin Sinnanci da abin ya shafa, mutanen kasashen waje sun iya neman shiga kwalejoji da jami'o'i iri daban daban na kasar Sin.

Mu Xiaolong, wani dan kasar Amurka, ya shiga jarrabawar HSK saboda dalilin da aka ambata a baya, ya ce,

'dalilan da suka sa na shiga jarrabawar HSK su ne, da farko, ina fata zan gano matsayina a fannin Sinnanci, da kuma abubuwan da nake bukatar in kyautata su; na biyu, jarrabawar HSK jarrabawa ce da gwamnatin kasar Sin ta shirya, in ina son in yi karatu in sami digiri na 2 a kasar Sin, ana bukatar takardar shaidar matsayin Sinnanci na 6.'

An ba da karin haske cewa, a shekarun baya da suka wuce, mutanen waje sun koyi Sinnanci don share fage ga yin karatu ko zama ko aiki a kasar Sin, a maimakon nuna sha'awa kawai. Lee Moon-kyu, dan kasar Korea ta Kudu ya bayyana cewa, neman samun takardar shaidar matsayin Sinnanci ba ma ya nuna maki da aka samu a fannin yin karatu a kasar Sin kawai ba, har ma ya taimakawa neman samun aikin yi a nan gaba, ya ce, 'yanzu 'yan kasar Korea ta Kudu masu yawa sun iya Sinnanci, masana'antun kasar Korea ta Kudu sun zakulo wasu mutane da ko sun iya Sinnanci ko a'a bisa makin jarrabwar HSK da aka samu.'

Babban dalilin da ya sa jarrabawar HSK ta sami amincewa sosai shi ne saboda bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri da kuma kara yin mu'amala da kasar Sin take yi da kasashen waje, ta yadda ya sa ana kara yin amfani da Sinnanci.

Don sa kaimi kan mutanen waje da su koyi Sinnanci da fahimtar al'adun kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin yabo ga mutanen da suka samu maki mai kyau a cikin jarrabawar HSK.

A lokacin da mutane suke kara shiga jarrabawar HSK, a sa'i daya kuma, masu shiga jarrabawar HSK daga wurare daban daban na duniya sun gabatar da cewa, da kyar jarrabawar HSK ta iya biyan bukatunsu, saboda sun zo daga wurare daban daban na duniya, ayyukansu sun sha bamban, kuma shekarunsu na haihuwa sun sha bamban. Don daidaita wannan batu, hukumar kasar Sin da abin ya shafa tana nazarin yin jarrabawar HSK don wurare daban daban na duniya, kamarsu yankin Amurka ta Arewa da Japan da Korea ta Kudu.

An labarta cewa, don kara kyautata amfanin jarrabawar HSK, kasar Sin ta yi shirin gabatar da jarrabawa a fannonin kasuwanci da yawon shakatawa da aikin sakatare.

Idan kana son kara samun labaru game da jarrabwar HSK, to, za ka bude shafin internet na www.hsk.org.cn.(Tasallah)