Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-12 10:48:37    
Kasar Iran tana son yin shawarwari ba tare da kowane sharadi ba kan sabon shirin da kasashe 6 suka bayar

cri
A ran 11 ga wata Ali Larijani, sakataren kwamitin koli na tabbatar da kwanciyar hankali na kasar Iran kuma wakilin farko na yin shawarwari kan maganar nukiliya ta Iran wanda ke yin ziyara a kasar Masar ya jaddada a birnin Alkahira cewa, kasar Iran tana son yin shawarwari ba tare da kowane sharadi ba kan sabon shirin daidaita maganar nukiliya ta Iran da kasashe 6 suka bayar, amma ba za ta amince da duk wata barazanar da aka yi mata ba.

Mr. Larijani ya ce, wannan sabon shirin da kasashe 6 suka bayar yana kunshe da wasu "matakai masu yakini", amma har yanzu ba a bayyana ra'ayoyinsu a bayyane ba kan muhimmiyar maganar da ke shafar aikin tace sinadarin uranium, dole ne a tabbatar da wannan magana yadda ya kamata.

Mr. Larijani ya jaddada cewa, kasar Iran ta raya shirin nukiliya domin ayyukan zaman lafiya kawai, ba za ta yi barzana ga sauran kasashen duniya ba. Kasar Iran tana maraba da yin shawarwari ba tare da kowane sharadi ba a tsakaninta da bangarorin da abin ya shafa.

A wannan rana kuma, Hamid Reza Asefi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran ya ce, gwamnatin kasar Iran tana ganin cewa za ta iya amincewa da wasu abubuwan shirin da kasashe 6 suka bayar, amma ya kamata a ci gaba da kyautata wasu abubuwan wannan shiri. A waje daya kuma, kasar Iran tana bukatar isashen lokaci domin duba abubuwan wannan sabon shiri, sannan kuma za ta iya bayar da ra'ayoyinta. Amma Mr. Asefi bai ambata abubuwan da ya kamata a kyautata su ko a shafe su ba. (Sanusi Chen)