Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-08 14:52:44    
Kasar Iran ta yi kira ga kasar Amurka da ta canja manufarta, da kuma ingiza shawarwarin bangarori biyu

cri
Ran 7 ga wata, Mr. Ali Larijani, babban wakilin shawarwarin nukiliya na kasar Iran, kuma sakataren babban kwamitin tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta canja manufarta mai kuskure gare kasar Iran, domin ingiza aiwatar da shawarwarin banbarori biyu lami lafiya.

A wannan rana a lokacin da Mr. Larijani ya gana da maneman labaru ya ce, a da kasar Amurka ta taba yin kuskure da yawa, idan za ta iya canja manufarta, to ba za a samu matsala ba a tsakaninsu wajen shawarwarin.

A wannan rana, Mr. Sean McCormack, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Amurka ya ce, tilas ne kasar Iran ta daina ayyukan urainium mai inganci a cikin shawarwarin nan gaba, sabo da wannan shi ne muhimmin shardi na shawarwarin.

A sa'i daya kuma,Mr. Javier Solana, muhimmin wakilin kungiyar tarayyar kasashen Turai mai kula da harkokin waje da manufar kwanciyar hankali, wanda ke yin ziyara a kasar Jamus ya bayyana cewa, babu cikas ta hanyar siyasa wajen warware matsalar nukiliya ta kasar Iran, ya nuna kyakkyawan fata ga makoman warware matsalar nan. A wannan rana kuma, Mr. Sergei Lavrov, ministan harkokin waje na kasar Rasha ya bayyana cewa, sai a lokacin da kasar Iran ta karya yarjejeniyar hana barbazuwar makaman nukiliya, kasar Rasha za ta goyon bayan kwamitin sulhu na M.D.D. da a sanya takunkumi ga kasar Iran. (Bilkisu)