Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-02 19:42:15    
Wasannin Olympic na Beijing ya dora muhimmanci kan ba da ilmin Olympic

cri

Bisa shirin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin suka tsara, an ce, za a ba da ilmin Olympic tsakanin matasa miliyan dari 4 a duk yankin kasar Sin a shekarar da muke ciki, domin haka, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin za ta kafa makarantu fiye da 500 wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic a duk kasar a wannan shekara.

Ainihin Olympic shi ne aikin ba da ilmi. Matasa su ne makomar duniyarmu, haka kuma makomar Olympic. Ba da ilmi tsakaninsu yana da muhimmanci sosai a fannin bunkasuwar wasannin Olympic da zaman al'ummar kasa. Kamar yadda shugaban makarantar midil ta 9 ta Beijing Mr. Ma Baosheng ya ce, wannan dukiya ce mai daraja: 'za mu ba da kayayyakin tarihi a fannin ba da ilmin Olympic ga wasannin Olympic na Beijing ta hanyar kafa makarantu wadanda abin koyi ne a fannin ba da ilmin Olympic. Za mu ba da gudummowarmu ga kasar Sin da Beijing da kuma dukan wasannin Olympic.'(Tasallah)


1  2  3