A ran 1 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya bayyana cewa, kasar Iran ta riga ta shirya domin yin shawarwari da kasar Amurka, amma ba za ta yi la'akari da bukatar kasarta, wato ba za ta daina ayyukan tace sinadarin Uranium ba.
A ran nan, Mottaki ya bayyana wa kafofin watsa labaru cewa, kasar Iran ta yi maraba da yin shawarwari bisa sharadi mai adalci, amma ba za ta sadaukar da hakkinta na nukiliya ba. Ya ce, kasar Iran ba za ta sadaukar da hakkinta na nukiliya bisa dokokin duniya da yarjejeniyoyin da abin ya shafa ba, amma tana son yin shawarwari da sassan da abin ya shafa bisa wani tsari mai adalci.
Mottaki ya ci gaba da cewa, babu wata shadar da ke cewa, kasar Iran tana kokarin kera makaman nukiliya, sabo da haka kasar Iran ba ta da shirin daina ayyukan nikiliya ba.(Danladi)
|