|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-05-31 17:59:45
|
 |
Kasar Iran za ta sake aiwatar da shawarwarin makamashin nukiliya
cri
Ran 30 ga wata a birnin Putrajaya, cibiyar hukuma ta kasar Malaysia, Mr. Manouchehr Mottaki, ministan harkokin waje na kasar Iran ya bayyana cewa, kasar Iran ta shirya ta shirya sosai, domin sake aiwatar da shawarwari da bangarori daban daban da ke nasaba kan matsalar nukiliya ta kasar Iran. A wannan rana kuma, shugaba Bush na kasar Amurka ya buga waya ga shugabannin kasashen Rasha, da Faransa, da kuma Jamus, domin samun goyon baya a cikin shawarwarin bangarori 6 kan matsalar nukiliya ta kasar Iran da za a shirya.
A gun taron watsa labaru da aka shirya bayan rufewar taron NAM-COB na matsayin ministoci, Mr. Mottaki ya bayyana cewa, kasar Iran tana son sake aiwatar da shawarwarin matsalar nukiliya da bangarori daban daban da ke da nasaba, kuma shawarwarin zai yi tattaunawa kan nufin kasar Iran nan gaba. Kan ra'ayin kasar Iran, Mr. Tony Snow, kakakin fadar gwamnatin kasar Amurka ya nuna maraba, kuma yana fata shawarwarin zai iya samu sakamako mai kyau.
A wannan rana, Mr. Bush, shugaban kasar Amurka ya buga waya ga Mr. Putin, shugaban kasar Rasha, da Mr. Sirak, shugaban kasar Faransa, , da kuma madam Merkel, firayin ministan kasar Jamusin daya bayan daya, inda da suka yin tattaunawa kan warware matsalar nukiliya ta kasar Iran, da kau da bambancin da ke kasancewa a tsakanin bangarori daban daban kan wannan matsalar. (Bilkisu)
|
|
|