Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-31 15:26:10    
Shugaban kasar Columbia Alvaro Uribe

cri

Shugaban kasar Columbia na yanzu Alvaro Uribe ya ci babban zaben da aka yi a ran 28 ga wata, bisa yawan kuri'un da ya samu fiye da kashi 60 cikin dari, sabo da haka ya sake darewa a kan karagar shugaban kasar. Daga baya kuma Uribe ya bayyana cewa, zai ci gaba da daukar kwararan matakai domin inganta bunkasuwar tattalin arziki da sa kaimi ga dakaru masu yin adawa da gawamnatin kasar musamman ma kungiyar FARC da su yi shawarwari tare da gwamantin don neman samun zaman lafiya a cikin kasar.

An haife Alvaro Uribe a ran 4 ga watan Yuli na shekara ta 1952, a cikin birnin Medelli, birni mafi girma na biyu a cikin kasar Columbia. Lokacin da yake makaranta, Uribe ya yi matukar kokari wajen karatu, kuma ya taba karatu a sashen dokoki na jami'ar Antioquia ta kasar Columbia, a cikin shekara ta 1970. ya samu digiri na dakta wajen ilmin dokoki da siyasa. Daga baya kuma ya shiga jami'ar Harvard ta kasar Amurka domin kara ilminsa, kuma ya samu digiri na MBA. Daga shekara ta 1998 zuwa 1999, ya taba zama furfesa a matsayin bako a cikin jami'ar Oxford. Sabo da wadannan abubuwan da ya taba yi, ba kawai ya iya turanci sosai ba, har ma ya yi hegen nesa wajen raya tattalin arzikin kasar Columbia.


1  2  3