Ran 22 ga wata, Hamid-reza Asefi kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Iran ya zargi maganar suka da Madam Condoleezza Rice babbar sakatariyar kasar Amurka ta yi ga kasar Iran, ya ce kasar Amurka ta yi rikici da gangan a kan batun nukiliya.
Bisa labarin da muka samu, Asafi yana tsamani nufin Rice shi ne don "ba da mugun tasiri ga taron da kasashen Amurka, Rasha, Sin, Faransa da Jamus za su yi don tattauna batun nukiliya." Kuma ya zargi kasar Amurka ta bayar da labari na karya da gangan don neman bata hadin gwiwar da kasar Iran da Kungiyar makamashin nukiliyar duniya za su yi. Asefi ya jaddada cewa, kasar Iran ba za ta daina tafiyar da shirin nukiliya ba.
|