Ran 21 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Iran Hamid-Reza Asefi ya ce, kasar Amurka ba ta yi alkawarin ba da tabbaci ga zaman lafiyar kasar Iran ba maras tasiri ne.
Kakaki Asefi ya yi wannan magana a taron manema labaru da aka yi a Teheran. Ya ce, a da kasar Amurka ba ta cika wai alkawarin da ta yi, shi ya sa kasar Iran tana tsamani wannan tabbacin zaman lafiya maras ma'ana ne. Asefi ya nuna cewa, duk matakan da kungiyar kawancen Turai ba za su sa kasar Iran ta daina yin binciken nukiliya.
|