Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-21 17:06:32    
Kasar Iran za ta amince da fatan siyasa na daidaita maganarta ta nukiliya ta hanyar diplomasiyya

cri
A ran 20 ga wata, Manouchehr Mottaki, ministan harkokin waje na kasar Iran wanda ke yin ziyara a kasar Kuwait ya jaddada cewa, idan ya kasance da fatan siyasa na daidaita maganar nukiliya ta Iran ta hanyar diplomasiyya ciki har da a hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa, to, gwamnatin Iran za ta yarda da amince da irin wannan fatan siyasa.

A gun wani hadadden taron manema labaru da Mottaki da Sheikh Mohammed Al-Sabah, mataimakin firayin minista kuma ministan harkokin waje na kasar Kuwait suka shirya tare, Mr. Mottaki ya ce, ya riga ya sanar da halin da ake ciki yanzu game da maganar nukiliya ta Iran ga shugabannin kasar Kuwait. Mr. Mottaki ya ce, kasar Iran tana da ikon aiwatar da shirinta na nukiliya. Game da matsayin da kasar Iran take bi kan wannan magana shi ne, neman wani cikakken shirin da bangarori daban-dabam dukkansu za su amince da shi, kuma za a iya kawar da damuwar da wasu kasashe suke ji kan wannan magana a kai a kai. (Sanusi Chen)