A ran 15 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Iran Manouchehr Mottaki ya bayyana cewa, kasar Iran za ta ki yarda da ko wace shawarar da kungiyar EU ta gabatar mata domin bukatar kasar Iran ta daina ayyukan tace sinadarin Uranium.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Irna na kasar Iran ya bayar, an ce, Malam Mottaki ya yi wannan bayani ne a yayin da yake ganawa da jakadun Ingila da Faransa da kuma Jamus da ke kasar Iran a ran nan. Ya ce, ko wace irin wannan shawara ba ta kunshe da ko kwayar zarra daya ta gaskiya ba, kuma ba za ta zama mai karbuwa ba, sabo da haka kasar Iran za ta ki yarda da ita ba tare da wata-wata ba.(Danladi)
|