Ran 14 ga wata, a birnin Tehran, shugaban kasar Iran Mr. Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa, idan kasashen Turai sun tanadi bukatar kasar Iran da ta daina harkokin nukiliya cikin lumana a cikin shawararsu, to, kasar Iran ba za ta amince da irin wannan shawara ba.
An labarta cewa, kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suna tsara sabuwar shawara kan batun nukiliya na kasar Iran, inda suka bukaci kasar Iran da ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya, ta kuma daina harkokin tace sinadarin uranium, in ba haka ba, mai yiwuwa ne za a haddasa takunkumi. An yi kiyasta cewa, jami'an ma'aikatan harkokin waje na wadannan kasashe 3 da Mr. Javier Solana, babban wakilin kawancen kasashen Turai mai kula da manufar harkokin waje da zaman lafiya za su yi tattaunawa kan wannan sabuwar shawara a ran 15 ga wata.(Tasallah)
|