Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-05 19:31:47    
Manyan mawaka guda biyu na zamanin da na kasar Sin wato mawaka Li Bai da Du Fu na daular Tang

cri

Li Bai

Daular Tang da ke tsakanin shekarar 618 zuwa shekarar 907, lokaci ne da kasar Sin ta sami ci gaba sosai da sosai wajen tsara rubutattun wkoki. A tarihin adabin kasar Sin, mutane su kan kiransu da cewar, "Lidu" don wakiltar babbar nasarar da aka samu wajen tsara rubutattun wakoki a daular Tang. "Li" shi ne Li Bai da ke da mashahurin suna a duniya wajen tsara rubutattun wakoki kuma ake kiransa da cewar wai shi ne dodo mai ban al'ajabi, "Du" shi ne Du Fu da ake kiransa da cewar kwararren mutum wajen tsara rubutattun wakoki.

Li Bai da Du Fu dukansu sun yi zama ne a karni na 8 da daular Tang ta sami wdatuwa sosai. Li Bai ya girmi Du Fu da shekaru 11 da haihuwa. An haifi Li Bai a wani karamin gari na jihar Xinjiang da ke iyakar kasar Sin, amma Du Fu jika ne ga mashahurin mawaki mai suna Du Shenyan. Zaman rayuwar Li Bai da Du Fu kusan iri daya ne a lokacin da suke kanana har suka zama samari. Suna da kishin karanta littattafai da yawa, kuma suna da sha'awa sosai wajen yin zane-zane da rera wakoki, har da hawan dawaki da yin wasan takobi. Sun taba yawon shakatawa a wurare daban daban da yawa a kasar Sin, kuma sun rubuta wakoki da yawa da suka bayyana halin da ake ciki a muhallin halittu.

Du Fu

Li Bai da Du Fu suna da bambancin ra'ayi sosai wajen zaman rayuwa, sa'anan kuma wajen halayen musamman na rubutattun wakokinsu. Li Bai ya yi abubuwa yadda ya ke so kawai, kuma ya yi kyamar wadanda suke da ikon mulki da arziki, kuma an iya ganin halin musamman da na jarumtaka da ya nuna da dai sauransu, shi ne mawakin da ke da halayen musamman masu ban sha'awa sosai a tarihin adabin kasar Sin. Li Bai yana da tunani mai ban mamaki a cikin rubutattun wakokinsa, ya yi amfani da maganganu masu sa ran alheri da faranta rai yadda ya ga dama a lokacin da ya rubuta wakokin da suke jawo sha'awar mutane sosai. Alal misali, a cikin wata wakar, ya rubuta cewa, hanyar da ke lardin Schuan na da wuyar wucewa, wuyar kamar yadda wuyar da ake gamuwa da ita wajen hawan sararin samaniya. A cikin wata waka daban da ya rubuta, ya bayyana cewa, " Ko ba ka ganin ruwan da ya sauko daga sararin samaniya, kuma ta malala har zuwa teku ba tare da komawa ba". Ya kuma rubuta cea, "ruwa ya malala har ya sauko daga sama da mita dubu, ana shakka cewa, wai saukar nan saukar kogin azurfa ne daga sararin samanicya" Mutanen da suka zo daga bayansa suna yadadda duk wadannan jimloli da sauran jimlolin wakokin da ya rubuta sosai.

Yawan wakokin da Li Bai ya rubuta ya kai dari 9 tare da bayanai da yawansu ya kai 60 ko fiye wadanda suke kunshe da abubuwa masu yawan gaske tare da samfurorin rubuc-rubuce masu yawa, sa'anan kuma suna da halayen musamman sosai da ba a taba gani ba har zuwa yau. Wasu shahararrun mawaka na kasar Sin da ke bayansa sun sami babban tasiri sosai daga wajensa, an kuma fasara wakokinsa da harsuna da yawa kamar su " Harshen Ingilishi da na Rashanci da Janananci da Jamusanci da sauransu.

Wakokin Du Fu na da bambanci sosai da na Li Bai. Du Fu ya hada da wakoki da hakikanan abubuwa da suka faru a zamantakewar al'umma da zaman ryuwarsa sosai da sosai, ya rubuta wakoki da yawa dangane da wahalolin da jama'a suke sha a lokacin yake-yake, ya bayyana yadda daular Tang take tabarbarewa sosai daga wadatuwa bayan yake-yaken da aka yi a cikin shekaru fiye da 20. Saboda haka, an bayyana cewa, wakokin da Du Fu ya rubuta su ne wakokin tarihi. Ya taba rubuta cewa, " Nama ya rube har ya yi wari sosai a cikin gidajen masu sukuni, amma a kan hanyar da akwai kasusuwan mutane.

Yawan wakokin da Dufu ya rubuta ya kai 1400 ko fiye. Wadanda suke kunshe da abubuwa da yawa, kuma suke ba da tasiri sosai ga mutanen da suka zo daga bayansa.(Halima)