Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-03 16:53:16    
Kasar Habasha tana son karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin kan raya 'yan kwadago

cri
A ran 2 ga wata, shugaban kasar Habasha Girma Wolde Giorgis ya bayyana cewa, kasar Habasha tana son karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin kan raya 'yan kwadago.

Yayin da yake ganawa da tsohon mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin kuma shugaban kungiyar sada zumunta tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen Afirka wanda ke yin ziyara a kasar, Girma ya ce, ya yi wa kasar Sin godiya da ta bayar da taimako ga kasar Habasha a fannin raya 'yan kwadago, kuma yana fatan bangarorin biyu za su kara yin hadin kai a wannan fanni.

Daga wajensa Yang Fuchang ya bayyana cewa, a cikin shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta kara karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka kan raya 'yan kwadago domin ba su taimako wajen samun dauwananniyar ci gaba kan tattalin arziki. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da bayar da gudummowarta kan horar da 'yan kwadago ga Afirka.(Kande Gao)