Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 16:13:17    
Shugabannin kasashen Sin da Kenya sun yi shawarwari tsakaninsu

cri

A ran 28 ga wata, a fadar gwamnatin kasar Kenya, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Kenya Mwai Kibaki. Bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayoyinsu kan dagantakar da ke tsaknin bangarorin biyu da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu.

Kafin shawarwarin, Kibaki ya shirya gaggarumin bikin maraba da zuwan Hu Jintao da hannu biyu.

Hu Jintao ya isa birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya ne a ran 27 ga wata don fara kai wa kasar ziyarar aiki. Bayan da ya isa filin jirgin sama, ya yi jawabi a rubuce, cewa tun da can har zuwa yanzu, kasashen Sin da Kenya sun raya huldar da ke tsakaninsu lami lafiya, bangarorin 2 sun dinga karfafa da zurfafa hadin gwiwar abokantaka da ke tsakaninsu a dukan fannoni, sun kara yin tattaunawa da taimakon juna kan harkokin duniya, da kiyaye moriyar bai daya nasu da kuma kasashe masu tasowa. Ya yi imanin cewa, ziyarar da ya yi a wannan gami zai ba da taimako wajen karfafa zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashen 2 da zurfafa hadin gwiwar abokantaka da ke tsakaninsu.(Kande Gao)