Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-28 08:46:04    
Hu Jintao ya sauka Nairobi ya fara ziyarar Kenya

cri
Ran 27 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya sauka birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, inda ya fara ziyarar aiki, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Kenya ya yi masa.

A cikin jawabin da ya yi a rubuce a filin jirgin sama, Mr. Hu ya bayyana cewa, a shekarun nan da suka wuce, a karkashin shugabancin shugaba Mwai Kibaki, gwamnati da jama'ar kasar Kenya sun kiyaye kwanciyar hankali na zaman al'ummar kasar da kuma hadin kan kabilu cikin himma da kwazo, sun kara karfin raya sha'annoni daban daban, sun kuma himmantu ga kwanciyar hankali da dinkuwar yankin da suke ciki, ta haka, sun sami yabo sosai.

Mr. Hu ya kara da cewa, tun da can har zuwa yanzu, kasashen Sin da Kenya sun raya huldar da ke tsakaninsu lami lafiya, bangarorin 2 sun dinga karfafa da zurfafa hadin gwiwar abokantaka da ke tsakaninsu a dukan fannoni, sun kara yin tattaunawa da taimakon juna kan harkokin duniya, da kiyaye moriyar bai daya nasu da kuma kasashe masu tasowa. Ya yi imanin cewa, ziyarar da ya yi a wannan gami zai ba da taimako wajen karfafa zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashen 2 da zurfafa hadin gwiwar abokantaka da ke tsakaninsu.(Tasallah)