Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-27 22:00:41    
Hu Jintao ya bayar da jawabi kan yadda za a kara raya dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 27 ga wata da safe, agogon Najeriya, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyara a lokacin a kasar Najeriya ya bayar da wani jawabi mai lakabi haka: "Yin kokari tare domin bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka bisa manyan tsare-tsare" a zauren majalisar dokokin kasar Najeriya, inda ya bayar da manufofi da ra'ayoyi na kasar Sin wajen raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka.

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A cikin ziyararsa ta farko da Mr. Hu ya yi a shekarar nan ya zabi kasashen Morocco da Najeriya da Kenya wadanda suke wakiltar kasashen arewacin kasashen Afirka da yammacin kasashen Afirka da gabashin kasashen Afirka wannan yana da cikakkiyyar alama cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka. A cikin farko jawabinsa ba tare da boye kome ba Mr. Hu ya bayar da burinsa na yin ziyara a kasashen Afirka. Mr. Hu ya ce, "Burin da nake son cimmawa a cikin wannan ziyara shi ne, kara fahimtar Afirka da sanin Afirka da koyi da Afirka. Sannan kuma mu gaji zumuncin gargajiya da ke kasancewa a tsakaninmu da kara wa juna fahimta da yin hadin guiwar moriyar juna da neman samun bunkasuwa tare domin raya sabuwar dangantakar abokantaka tare da kasashen Afirka."

Mr. Hu ya nuna cewa, a cikin halin da ake ciki yanzu, kasashen Duniya suna dogara kan juna sosai, dangantakar moriyar juna da ke kasancewa a tsakaninsu tana samun karfafuwa kwarai.

A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya bayar da ra'ayoyi 4 kan yadda za a gaji zumuncin gargajiya da ke kasancewa a tsakanin Sin da kasashen Afirka da kuma raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Mr. Hu ya ce, "Kara fahimtar juna kan harkokin siyasa da kara yin hadin guiwar moriyar juna kan tattalin arziki da kara yin koyi da juna kan al'adu da kuma kara yin hadin guiwa kan harkokin tabbatar da zaman lafiya."

Lokacin da yake bayyana wadannan ra'ayoyi 4 filla filla, Mr. Hu ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa kasashen Afirka taimako bisa namijin kokarinta. Wannan manufa ce da gwamnatin kasar Sin ke dauka ba tare da kasala ba.

A sa'i daya kuma, Hu Jintao ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara zuba kudade domin halartar ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afirka da ke karkashin jagorancin M.D.D., kuma za ta kara sa kaimi ga sauran kasashen duniya da su kara mai da hankali kan maganar neman bunkasuwa da maganar yadda za a daidaita batun rashin cikakken ikon wakilci na kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka a M.D.D.

Bugu da kari kuma, Hu Jintao ya bayyana halin neman bunkasuwar tattalin arziki da kasar Sin ke ciki da burin neman bunkasuwa da kasar Sin take nema. Mr. Hu ya ce, har yanzu, kasar Sin kasa ce mai tasowa, kuma ta dade tana zangon farko na zaman al'ummar gurguzu. Lokacin da jama'ar kasar Sin suke neman bunkasuwar kasarsu, za su daga tutar tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa da yin hadin guiwa da kasashen waje cikin lumana. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar 'yantattar da kasa mai zamna kanta cikin lumana kan harkokin waje da hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, kuma za ta dinga aiwatar da shirin bude wa kasashen waje kofa domin neman bunkasuwa tare da moriyar juna da kasashen waje. Jama'ar kasar Sin za su hada kai da jama'ar sauran kasashen duniya domin kafa wata duniyar da ke cike da zaman lafiya mai dorewa da bunkasuwa da jituwa. Mr. Hu ya ce, "Abin gaskiya ya riga ya tabbatar kuma zai ci gaba da tabbatar da cewa, kasar Sin tana neman bunkasuwa bisa ka'idojin bude wa kasashen waje kofa da yin hadin guiwa da kasashen waje cikin lumana. Bunkasuwar kasar Sin ba za ta kawo wa kowane mutum barzana ba, amma za ta kawo duk duniya damar neman bunkasuwa."

Bayan da ya yi jawabi, 'yan majalisun dokokin kasar Najeriya bi da bi ne suka yaba wa jawabin da Mr. Hu ya yi. (Sanusi Chen)