Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-27 18:00:05    
Kasar Sin da Najeriya sun bayar da wata hadaddiyar Sanarwa

cri

Bisa gayyatar da shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Najeriya ya yi masa ne, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai wa kasar Najeriya ziyarar aiki tun daga ran 26 zuwa ran 27 ga wata. Lokacin da yake yin ziyara a kasar Najeriya, kasashen biyu sun bayar da wata Hadaddiyar Sanarwa, inda suka tsai da kudurin kara yin hadin guiwa a wasu sabbin fannoni domin ciyar da dangantakar abokanta da ke tsakaninsu gaba bisa manyan tsare-tsare.

Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun yi farin ciki sosai ga cigaban dangantakar hadin guiwa irin ta sada zumunta a tsakaninsu da aka samu cikin hali mai dorewa a cikin shekaru 35 da suka wuce. Dukkansu sun bayyana cewa, hadin guiwar tattalin arziki a tsakanin Sin da Najeriya tana da boyayyen karfi sosai da makoma mai haske. Bangarorin biyu sun bayyana cewa za su kara yin hadi guiwa wajen aikin gona da sana'o'in samar da wutar lantarki da raya ayyukan yau da kullum da makamashin halittu da sadarwa da dai sauransu. Sannan kuma, bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su kara hada kan juna kan harkokin duniya bisa tunanin kara raya dangantakar abokantaka da ke kasancewa a tsakaninsu domin bayar da kokarin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa da kafa wata duniyar da ke cike da jituwa da zaman lafiya da bunkasuwa.

Bugu da kari kuma, bangarorin biyu sun yaba wa dangantakar hadin guiwa irin ta sada zumunta da ke kasancewa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Sun kuma bayyana cewa, za su yi kokari tare wajen raya sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke kasancewa tare da amincewa da juna kan harkokin siyasa da zaman daidai wa daida da yin hadin guiwar tattalin arziki da cin nasara tare da kuma yin musanye-musanyen al'adu a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Sannan kuma, bangaren kasar Najeriya ya jaddada matsayin bin manufar Sin daya tak da take bi, kuma yana goyon bayan dukkan kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi domin neman dinkuwar duk kasar Sin. Bangaren kasar Sin ya yaba wa wannan matsayin da kasar Najeriya take bi sosai. (Sanusi Chen)