Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 11:11:29    
Mr. Hu Jintao ya gana da Mr. Sultan Bin Abdul-Aziz, yarima mai jiran gado na kasar Saudi Arabia, kuma ya yi shawarwari da shugaban taron ba da shawara na kasar

cri

Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, ran 23 ga wata a birnin Riyadh, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin, wanda ke yin ziyarar aiki ga kasar Saudi Arabia ya gana da Mr. Sultan Bin Abdul-Aziz, yarima mai jiran gado, kuma mataimakin firayin ministan kasar, bayan haka kuma ya yi shawarwari da Mr. Saleh Abdullah Homaid, shugaban taron ba da shawara na kasar Saudi Arabia.

A lokacin da Mr. Hu Jintao yake ganawa da Mr. Sultan ya ce, kasar Sin tana yin kokari kan bunkasa tsare-tsaren dangantakar hadin kai da ke tsakaninta da kasar Saudi Arabia, tana fatan kara yin cudanya, da kara fahimtar juna wajen siyasa, da samun moriyar juna da hada kai, kuma da bunkasa tare wajen tattalin arziki, da kuma nuna girmama da fahimtar juna wajen al'adu.

Mr. Sultan ya ce, jama'ar kasashen Saudi Arabia, da Sin suna kaunar zaman lafiya, kuma dangantakar da ke tsakanin kasashen Saudi Arabia da Sin ita ce abin koyarwa wajen dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa. Bangaren Saudi Arabia yana fata kasashen nan biyu za su karfafa hadin kansu a filayen tattalin arziki, da ciniki, da kuma fasaha, da dai sauransu.

A lokacin da Mr. Hu Jintao ke yin shawarwari da Mr. Homaid, ya jadadda cewa, ya kamata kasashen Sin da Saudi Arabia su ingiza bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarorin nan biyu ta yin tattaunawa da cudanya iri-iri, domin ba da sabon taimako wajen samar da ci gaban wayin kai na jama'a, da kuma kafa duniya mai daidaituwa. (Bilkisu)