Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-24 10:25:11    
Mr Hu Jintao da Mr Wen Jiabao sun nemi a kiyaye lafiyar Sinawan da ke zama a kasashen waje

cri
Shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayim ministan kasar Wen Jiabao bi da bi ne suka bukaci sassan da abin ya shafa a kwanan baya, don kiyaye lafiyar Sinawan da ke zama a tsibiran Soloman  wadanda suke shan tasirin hargitsin da ya faru a kasar da su taimaka. Tun daga ranar 22 ga wannan wata, bi da bi ne gwamnatin kasar Sin ta janye jikin Sinawan da ke shan wahalolin hargitsin a tsibiran Soloman .

A ran 23 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao da ke yin ziyarar aiki a kasar Saudiyya ya ba da umurni ga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da ofishoshin jakadanci na kasar Sin da ke wakilci a Papua New Guinea da sauran kasashe don daukar matakai na kiyaye lafiyar Sinawan da ke zama a tsibiran Soloman   kuma  su yi iyakacin kokari ga taimaka musu wajen daidaita wahalolin.

Kwanan baya, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao shi ma ya ba da umurni ga ma'aikatar harkokin waje da sassan da abin ya shafa don mai da hankali sosai ga bunkasuwar wannan halin da ake ciki da kuma daukar matakan da suka wajaba don kiyaye lafiyar Sinawan da ke zama a tsibiran.(Halima)