Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 18:06:10    
Shugaba Hu Jintao da shugaba Bush sun yi shawarwari a tsakaninsu

cri

A ran 20 ga wata a white house wato fadar gwamnatin Amurka, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari a tsakaninsa da shugaba Bush na Amurka. Bangarorin 2 gaba dayansu sun bayyana cewa, bisa halin da ake ciki yanzu a duniya, kasar Sin da Amurka suna da babbar moriyar tarayya ta muhimman tsare-tsare, kuma suna da makoma mai haske wajen hadin gwiwarsu. Bangarorin 2 sun yarda da kyautata da kuma daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 bisa matsayin muhimman tsare-tsare kuma ta hanyar hangen nesa, da sa kaimi ga ciyar da dangantar hadin gwiwa mai amfani a tsakanin su a karni na 21 gaba, da kara samar da zaman alheri ga jama'ar kasashen 2 haka ma ga jama'ar kasashe daban- daban na duniya gaba daya.

Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, Sin da Amurka suna da babbar moriyar tarayya ta muhimman tsare-tsare kuma suna daukar alhakin tarayya bisa wuyansu a fannin kiyaye zamaan lafiyar duniya da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.

Mr. Bush ya yaba ra'ayin da Mr. Hu ya dauka kan dangantakar da ke tsakanin bangarorin 2. Ya ce, yawan fannonin da Sin da Amurka suke yin hadin gwiwa a tsakanin su sai kara karuwa yake a kowace rana.

Kan matsalar Taiwan, Mr. Hu ya bayyana cewa, Sin da Amurka suna da moriyar muhimman tsare-tsare ta tarayya wajen yin adawa da rukunin 'yan kawo baraka na Taiwan, da kiyaye zaman lafiya da zaman dorewa na mashigin tekun Taiwan.

Mr. Bush ya bayyana cewa, Amurka tana tsayawa kan manufar kasar Sin daya kawai a duniya, kuma ta fahimci dalilin da ya sa kasar Sin ta mai da hankali sosai kan matsalar Taiwan, kuma ba ta son ganin hukumar Taiwan da ta lahanta dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ta hanyar sauya halin da ake cikin yanzu a mashigin tekun Taiwan bisa gefe daya. (Umaru)