Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-21 16:43:27    
Mr. Hu Jintao ya gana da mataimakin shugaban kasar Amurka da shugaban wucin gadi na majalisar dattijai ta kasar

cri
Ran 20 ga wata, a birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Mr. Dick Cheney da shugaban wucin gadi na majalisar dattijai ta kasar Mr. Ted Stevens da kuma mai ba da taimako ga shugaban kasar a fannin harkokin tsaron kasa Mr. Stephen Hadley daya bayan daya.

Lokacin da yake ganawa da Mr. Cheney, Mr. Hu ya bayyana cewa, shugaba Bush da shi dukansu suna ganin cewa, kasashen Sin da Amurka kasashe ne da ke ba da muhimmin tasiri a duk duniya, suna da moriyar muhimman tsare-tsare bai daya a fannoni daban daban. A cikin sabon halin da ake ciki a yanzu, ya kamata bangarorin 2 su raya dangantakar hadin gwiwa mai amfani da ke tsakaninsu daga duk fannoni a cikin karni na 21, su gama kansu su ba da sabuwar gudummowa wajen sa kaimi kan zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma wadatuwa a yankin Asiya da tekun Pacific da kuma duk fadin duniya.

Daga nasa wajen kuma, Mr. Cheney ya ce, yana goyon bayan kafa huldar muhimman tsare-tsare a tsakanin kasashen Amurka da Sin.(Tasallah)