Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-19 16:58:16    
Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya fara ziyarar aiki kan kasashe biyar

cri

Bisa gayyatar da shugabannin kasashen Amurka, da Saudi Arabia, da Morocco, da Nijerya, da kuma Kenya suka yi masa ne ran 18 ga wata, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya bar birnin Beijing don fara ziyarar aiki kan wadannan kasashe 5. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara ga kasashen waje a shekarar da muke ciki. Yanzu, ga cikakken bayani:

Ana ganin cewa, a cikin harkokin waje na kasar Sin, dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ita ce daya daga dangantakar da ke tsakanin bangarori biyu da suka fi muhimmanci a duniyar yau. Wannan ziyarar aiki ta farko ce da Mr. Hu Jintao ya kai wa kasar Amurka bisa matsayinsa na shugaban kasar Sin. A taron manema labaru da aka shirya a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, Mr. Yang Jiechi, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana cewa,"Shugaba Hu Jintao zai yi musayen ra'ayoyi sosai da shugaba Bush da kuma sauran shugabannin kasar Amurka kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, da manyan matsalolin duniya da na shiyyoyi da ke jawo hankulan bangarorin nan biyu, kuma zai yi cudanya da mutane masu fito daga da'irori daban daban. Bayan haka kuma, shugaba Hu Jintao zai yi jawabi a jami'ar Yale, da kuma kungiyoyin sada zumunci na kasar Amurka, inda zai bayyana manufofin kasar Sin na ciki da na waje wajen ingiza yunkurin neman samun dauwamamen ci gaba, da kafa daidaituwar al'umma, da tsaya kan hanyar bunkasuwa cikin lumana, da kuma kafa daidaituwar duniya."


1  2  3