Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-13 21:25:31    
Sinnanci yana fuskantar hanyoyin sadarwar internet

cri

Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Sinnanci yana fuskantar hanyoyin sadarwar internet .

Wakilin Tashar internet mai sunan On Line ya ruwaito mana labarin cewa , Majalisar wakilan jama'ar Lardin Fujian yanzu tana duba shirin wata dokar shari'a , ta yadda za a yi amfani da sinnanci ta hanyar daidaici . Ina dalilin da ya sa aka gabatar da wannan batu ? Saboda A cikin 'yan shekarun da suka shige , an bullo da kalmomin Internet masu yawa wadanda ba su dace da dokar daidaitaccen sinnaci ba . Shi ya sa bayan da aka labarta cewa , majalisar Lardin Fujian ta tsara wannan shirin dokar , labarin ya jawo hankulan mutane kwarai da gaske .

Shi Jin , dalibar Jami'ar Jama'ar Sin tana son tadi da abonkanta ta hanyar sadarwar internet . Kullum tana buga keyboard da sauri . Kalmomin sinnaci da ta buga a shafin internet , ba a gane ma'anarta ba . A cikin litattafan da madaba'a

ta fitar , babu wadannan kalmomi . Alal misali ta kan yi amfani da 88 da ya wakiltar Byebye . Wannan a kan kiran harshn Internet .

Miss Shi ta ce , ina son harshen internet , saboda yana da sauki kuma yana da karfi , shi ya sa ya dace da mu matasa . Idan Shi Jin ta yi ma'amala da abokanta ta hanyar sadarwar internet kawai , ba laifi , kuma ba za ta jawo hankalin mutane ba . Amma duk da haka bayan da samari suka ingiza wadannan kalmomin internet su zama kalmomin baka tsakanin mutane , sai ya zama wani rikici . Yanzu a cikin matasa su kan tadi da kalmomin internet , har ma a cikin litattafan da aka buga a madaba'a akwai kalmomin masu yawa . Bugu da kari kuma a cikin kanun bayanin jarida akwai kalmomin . Wannan ya sa mutanen da ba su san harshen internet su sha wahalar mene ne suke nufi .

Miss Wang Min , akawunar wani kamfanin birnin Shanghai daya ce dake cikin masu shan wahalar harshen internet . Ta gaya wa wakilin Rediyon kasar Sin cewa, yanzu sinnacin da ake amfani bai dace da doka ba fiye da lokacin da . Wasu kalmomin internet ban gane ba . Alal misali funs da PK da sauransu ban gane ba mene ne nufinsu . Ni ba zan karbi wadannan kalmomi ba .

Yaduwar kalmomin internet ba kawai ta kawo damuwa ga balagai ba , har ma a cikin makarantun firamare , masu karatu su kan yi magana da kalmomin internet , Wani lokaci 'yan makaranta su kan rubuta gajeren bayani da kalmomin internet , har ma Malamai masu koyarwa ba su gane nufinsu ba. An yi ta yi haka , mutane masu yawa sun bayyana cewa , idan za a ci gaba da yada kalmomin internet , to , ko shakka babu za a gamu da wahaloli masu yawa fiye da lokacin da . Saboda haka hukumar kula da harshe da rubutu ta birnin Shanghai da Majalisar wakilan jama'ar Lardin Fujian sun tsara dokar sharia don hana amfanin kalmomin internet .(Ado )