Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-15 16:21:58    
Kafofin watsa labaru da masanan ilmi na kasashen waje suna kara lura da tarurrukan majalisu biyu na kasar Sin

cri

Labarun rufe tarurruka biyu na majalisu biyu na kasar Sin sun jawo hankulan kafofin watsa labaru da masanan ilimi na kasashen waje sosai, musamman ma batutuwan raya kauyuka na sabon salo da na Taiwan da shirin shekaru biyar na raya kasar Sin na 10 da aka tattauna a gun tarurrukan nan su ma sun sami martani sosai daga wajensu.

Kafofin watsa labaru na kasar Korea ta Kudu ta bayar da labarun rufe tarurrukan nan biyu daya bayan daya. Jarida " The Soul Economic Daily" ta nuna cewa, tarurrukan sun zartas da manufofi da dama dangane da bunkasa harkokin tattalin arzikir kasar Sin da zaman jama'arta nan da shekaru biyar masu zuwa, babban makasudinsu shi ne domin neman bunkasawa cikin zaman karko da daidaituwa. Jarida "Herald Economic Daily" ita ma ta ce, hanyoyi da wannan taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya nuna don neman daidaita matsalolin zaman rayuwar jama'a da na tattalin arziki sun yi duk tarurrukan yawa.

Kafofin watsa labaru na kasar Canada sun mai da hankali sosai ga tarurrukan nan biyu na kasar Sin. Jarida mai suna "Huanqiuhuabao" ta kasar ta buga sharhi cewa, nuna kulawa ga jama'a marasa matsayi mai rinjaye babban ma'auni ne da ake bi wajen tabbatar da wata gwamnati mai kishin jama'a, ko a'a.

Jaridar kasar Rasha da ake kira "Rossiskaya Gazeta" ta buga bayani a ran 14 ga wata cewa, tarurrukan kasar Sin biyu sun tsaida kudurai da ba a taba yi ba a da, ta yadda kasar Sin za ta kara daidaita matakai da take dauka bisa shiri da hanyoyi da take bi wajen yin kwaskwarima kan kasuwanni. (Halilu)