Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-14 20:00:47    
Kasar Sin ta rigaya ta zama wata kasa mai daukar alhakin dake bisa wuyanta yadda ya kamata

cri

A gun taron ganawa da manema labaru da aka shirya yau a nan Beijing, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya fadi cewa kasar Sin ta rigaya ta zama wata kasa mai daukar alhakin dake bisa wuyanta a duniya. Daga baya Wen Jiabao ya bayyana abubuwa guda l0 na gaskanta ra'ayinsa. Ya nuna, cawa yalwatuwa da zaman karko na kasar Sin sun kasance babban taimako ne ga zaman lafiya da wadata na duniya ; Kasar Sin ta riga ya samo wata hanyar raya kasa ta fuskar kimiyya a fannin yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli ; Ban da wannan kuma Wen Jiabao ya jaddada, cewa kasar Sin tana aiwatar da manufar samun wanzuwar zaman lafiya ba tare da tsangwama ba game da harkokin waje, kuma tana so ta yi zama cikin lumana tare da dukkan kasashe ; Kasar Sin tana aiwatar da manufar samun zaman jituwa da sada zumunta tsakaninta da kasashe makwabtanta ; Kasar Sin ana damawa da ita tare da  kiyaye tsarin kasashen duniya ce, kuma tana nan tana yin kokari tare da kasashen duniya wajen kafa sabon tsarin siyasa da na tattalin arziki na duniya ; Kazalika, Wen Jiabao ya furta, cewa Kasar Sin kasa ce dake tsayawa tsayin daka wajen kiyaye zaman lafiya na duniya,kuma har kullum takan tsaya kan matsayin shawo kai don shimfida zaman lafiya da kuma sa kaimi ga yin shawarwari game da maganar nukiliya ta Zirin Koriya, da maganar nukiliya ta Iran da dai sauran muhimman maganganu na kasashen duniya ; Dadin dadawa, Wen Jiabao ya fadi cewa kasar Sin ta kuma dauki ra'ayin hadin gwiwa ga tsaron kwanciyar hankali kan al'amuran da kan fafu kwatsam, ciki har da bala'in hallita da ya kan faru a duniya ; Kasar Sin ta tsaya haikan ta nuna kiyayya ga ' yan ta'adda da kuma danyen aiki habaka makaman nukiliya. Kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka bayan da aka shigar da ita cikin kungiyar WTO ; Kasar Sin tana himmantuwa wajen aiwatar da manufar yalwatatuwa ta shekaru dubu da M.D.D. ta fito da ita. A karshe dai Wen Jiabao ya karfafa magana, cewa kasar Sin tana aiwatar da bayyananiyar manufar tsaron kai. ( Sani Wang )