Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-14 11:03:04    
An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ta 10

cri

Wakilin Kamfanin dillancin labarum Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , ran 14 ga watan Maris da safe a nan birnin Beijing , An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ta 10 . Taron ya zartas da Shirye-shiryen raya tattalin arzikin kasar da zaman al'umman kasar a shekaru 5 masu zuwa da rahoton aikin gwamnati .

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin kasar Sin shekara-shekara zai kai kashi 7.5 cikin 100 . Kuma an tabbatar da makasudin rage yawan makamashin da za a kashe da rage yawan 'kazamin abubuwan da za a fitar . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kafa sababbin kauyyuka da hanzarta gyare-gyaren tattalin arziki da ciyar da yalwatuwar shiyya-shiyya cikin daidaici da kara karfin kirkiro mai ikon kai za su zama tsarin musamman da manyan ayyukan kasar Sin .

Rahoton aikin gwamnatin ya gabatar da cewa , za a soke kudin karatu da ba da ilmi ba tare da biya kudi ba a duk

kauyukan kasar Sin kuma an tsai da kudurin cewa , a wannan shekara yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 8 cikin 100 . (Ado)