Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-13 10:26:01    
An rufe taro na hudu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ta 10

cri

Ran 13 ga wata, an rufe taron shekarar nan na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wato hukumar koli da jam'iyyun siyasa da dama ke ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin wanda aka shafe kwanaki 11 ana yinsa a nan birnin Beijing. Taron ya gabatar da cewa, za a yi kokari sosai wajen cim ma shirin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da na zaman jama'arta nan da shekaru 5 mazu zuwa wato shirin shekaru biyar na 11.

Bisa kudurin siyasa da aka zartas a gun taron, an ce, ya kamata, a kara bunkasa aikin gona, a kara wa manoma kudin shiga mai yawa, a tabbatar wa manoma ikon dimokuradiyya, kuma a ingiza raya kauyuka irin na sabon salo don kawo fa'ida ga manoma miliyan darurruwa, haka zalika a kara kwarewa wajen yin kirkire-kirkire cikin cin gashin kai, a tsaya tsayin daka wajen yin adawa da 'yan a-waei na Taiwan da wadarin aikinsu da kuma dakile su, sa'an nan a yi kokari wajen ba da taimako don bunkasa hulda a tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan da tabbatar da dinkuwar kasar Sin baki daya.

Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ne ya shugabanci rufe taron. Manyan shugabannin kasar Sin kamar Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da sauransu sun halarci bikin rufe taron. (Halilu)