Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-10 19:26:27    
Kasar Sin za ta dauki matakai don sa kaimi ga masana'antu da su yi ayyukan sabuntawa cikin 'yanci

cri

A ran 10 ga wannan wata, mataimakin darektan kwamitin kula da harkokin raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin Zhang Xiaoqiang ya bayyana cewa, don raya kasar Sin da ta zama wata kasar da ke kokarin yin aikin sabuntawa, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai don sa kaimi ga masana'antu da su yi ayyukan sabuntawa cikin 'yanci.

Mr Zhang Xiaoqiang ya yi wannan furuci ne a gun taron ganawa da manema labaru da Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta shirya domin taronta na shekara shekara. Ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata muhallin manufofi na himmantar da masana'antu wajen yin ayyukan sabuntawa cikin 'yanci da kuma kara karfin zuba jari da kuma sa kaimi ga sassan da abin ya shafa da masana'antu da su kara saurin manyan ayyukan kimiyya da fasaha, kuma ta yi kokarin kafa dakunan gwaje-gwaje fiye da 100 na ayyukan kasa da kuma sa kaimi ga manyan masana'antu daruruka da su kafa cibiyar fasahohi don yin ayyukan sabuntawa cikin 'yanci.(Halima)