Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-09 21:17:14    
Zaunennen kwamitin NPC na kasar Sin zai kara sa ido kan aikace-aikacen gwamnati a fili

cri
A ran 9 ga wata, Mr. Wu Bangguo, shugaban zaunennen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a shekarar da muke ciki, zaunennen kwamitin majalisar zai ci gaba da sa ido kan muhimman batutuwa da maganganun da ke jawo hankulan jama'a sosai. A sa'i daya kuma, zai kara yin wannan aiki ne a fili.

A wannan rana da safe, a gun taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin, an saurari rahoton da Wu Bangguo ya gabatar a madadin zaunennen kwamitin majalisar. Mr. Wu ya bayyana cewa, a cikin shekarar da muke ciki, zaunannen kwamitin zai yi bincike kan yadda ake bin dokoki game da fannonin aikin gona da ikon mallakar fasaha da yin tsimin yin amfani da makamashin halittu da kuma aikin yin amfani da kasafin kudi da harkokin tattalin arziki. (Sanusi Chen)