Bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi ya zama muhimmin labarin da ke cikin manyan jaridun Hongkong da Macao da aka buga a ran 6 ga wata, kuma tsara tattalin arzikin wuraren biyu a cikin shiri na 11 na bunkasuwar tattalin arzikin da zaman al'ummar kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa ya fi daukar hankulan mutane.
Jaridar Wenhui ta Hongkong ta bayar da bayanin edita cewa, daftarin ka'idojin shirin ya jaddada cewa, ya kamata a tabbatar da matsayin Hongkong na cibiyar harkokin kudi da ciniki da sufuri ta duniya da kuma karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin Hongkong da babban yankin kasar Sin, wannan ya bayyana muhimmin matsayi na Hongkong a bangaren bunkasuwar kasar Sin baki daya, haka kuma ya nuna goyon bayan da gwamnatin tsakiya ta bai wa Hongkong.(Lubabatu Lei)
|