Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-06 16:54:16    
Kasar Sin za ta canja hanyar da take bi wajen bunkasa tattalin arzikinta

cri
Yanzu ana zaman taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato hukumar koli ta kasar a nan birnin Beijing. Wani babban batun taron nan shi ne dudduba tsarin ka'idojin shirin shekara biyar na 11 na bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman jama'a da kuma zartas da shi. Yayin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ke gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati a gun taron nan da aka yi a ran 5 ga wata, ya nuna cewa, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen canja hanyar da take bi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki, za ta nemi samun ci gaba mai dorewa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki ta hanyar tsimin albarkatu da kare muhalli. Ba ma kawai hanyar nan ta zama tunani mai muhimmanci ga yin ayyukan gwamnati ba, har ma ta sami amincewa daga wajen wakilai mahalartan taro da bangarori daban daban na kasar.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa a shekaru 1980, matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasa ya karu da sama da kashi 9 cikin dari a ko wace shekara, amma babbar hasarar da ta yi yayin da take bunkasa tattalin arziki da sauri a cikin sama da shekaru 20 da suka wuce, ita ce na farko gurbacewar muhalli, na biyu kuwa albarkatu da ta yi amfani da su sun karu da sauri. Malam Fu Yonglin, dan majalisar wakilan jama'ar kasa kuma shehun malamin jami'ar koyon aikin sufuri ta kudu maso yamma ya bayyana ra'ayinsa a kan wannan cewa, "manyan matsaloli da muke fuskanta a yanzu a fannoni biyu wato albarkatu da muhalli. Alal misali ko da yake yawan kudi da kasarmu ta samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP ya kai kashi 4.1 cikin dari bisa na duk duniya, amma yawan sumunti da kasarmu ta yi amfani da su ya kai kashi 47 cikin dari bisa na duk duniya. Haka nan kuma albarkatu masu muhimmanci kamar su filaye da ruwa da man fetur da hatsi da makamantansu sun zama kalubale mai tsanani da muke fuskanta yayin da muke neman samun ci gaba mai dorewa. "

Da ganin haka, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, a canja hanyar da ake bi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki. A cikin rahotonsa a kan ayyukan gwamnati, firayim minista Wen Jiabao ya bayyana cewa, "gwamnatin Sin ta yi haka ne sabo da mutsaloli da muke fuskanta wajen samun albarkatu da kare muhalli kullum sai kara tsanani suke yi. Kuma abun da ya kamata mu yi don neman raya zaman jama'a mai tsimin albarkatu da kare muhalli da kuma tabbatar da samun moriya cikin dogon lokaci. Ko da ya ke da kyar za a cim ma manufar nan, amma duk da haka muna cike da imani ga cim ma manufar nan."

Malam Theo De Hair, babban jami'in zartaswa na rukunin CAP GEMINI a kasar Sin wanda ya zo kasar Sin a cikin shekara daya da 'yan doriya, amma ya riga ya fahimci ayyuka da kasar Sin ke yi don neman raya zaman jama'a na sabon salo, yana fatan za a kara kokari sosai wajen yin ayyukan nan, yayin da ake aiwatar da shirin shekara biyar na raya kasa na 11. Ya ce, "tabbas ne, wannan shirin raya kasa zai samar mana da gurabe mafi kyau na zuba jari, da samun ci gaba mai dorewa. A ganina, nan da 'yan shekaru masu zuwa, kasar Sin za ta zama sabon sansani mai girma sosai da ake yin kirkire-kirkire a duniya." (Halilu)