Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-05 20:48:24    
Mr Hu Jintao ya dudduba rahoton gwamnati tare da mahalartan taron NPC

cri
Ran 5 ga wata da maraice, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin kuma dan majalisar wakilan jama'ar kasar da sauran shugabannin kasar sun yi tattaunawa a cikin kungiyoyin wakilansu bi da bi don dudduba rahoto kan ayyukan gwamnati.

An bude taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato taron NPC a nan birnin Beijing a ran 5 ga wata da maraice, inda firayim minista Wen Jiabao ya gabatar wa taron rahoto kan ayyukan gwamnati.

A cikin kungiyar wakilan jihar Tibet, Mr Hu Jintao ya jaddada cewa, don cim ma manufar bunkasa harkokin tattalin arziki da na zaman jama'a a cikin shekaru 5 masu zuwa, wajibi ne, a aiwatar da ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, a mayar da moriyar jama'a a gaban kome, a sami ci gaba mai dorewa cikin daidaituwa kuma daga duk fannoni , yayin da ake gaggauta bunkasa harkokin tattalin arziki da na zaman jama'a.

Yayin da Mr Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin yake dudduba rahoto kan ayyukan gwamnati a cikin kungiyar wakilai ta lardin Anhui, sai ya ce, ya kamata, a yi kokari sosai wajen kyautata tsarin tattalin arziki, a canja hanyar da ake bi wajen bunkasa tattalin arziki. (Halilu)