Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-05 18:03:42    
Manyan tarurruka biyu na wannan shekara za su bude sabon shafin zamanintar daSin, in ji kafofin yada labarai na Hongkong da Macao

cri
Kafofin yada labarai na Hongkong da Macao suna ganin cewa, taron shekara-shekara na majalisar wakilan dukan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da aka bude za su sa kaimi ga dukan al'ummar kasar Sin da kuma hada kansu wajen bude wani sabon shafin zamanintar da kasar Sin.

Jaridar Wenhui ta Hongkong ta bayar da bayanin edita cewa, 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa dubbai daga wurare daban daban na kasar Sin sun taru a birnin Beijing, ana imani da cewa, za su ba da shawarwari kamar yadda ya kamata, kuma za su kyautata tsarin ka'idojin raya kasa, za su kuma bayar da wani shirin taswira mai inganci don neman kara samun ci gaba a nan kasar Sin a shekaru biyar masu zuwa ko fiye.(Lubabatu Lei)