Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-05 17:19:36    
Ana mai da hankali kan batutuwan da ake fin yin tattaunawa a kan taruruka 2

cri

Yanzu, ana yin tarurukan shekara-shekara 2 na majalisar dokokin kasar Sin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da su kan jawo hankulan jama'ar kasar Sin. A gun tarurukan, wakilai da membobi suna da nauyin sa ido kan aikace-aikacen da gwamnati ta yi kuma da nauyin ba da shawarce-shawarcensu ga yunkurin neman bunkasuwar kasar. Sannan kuma za su tattauna wasu muhimman maganganun da ake gamuwa da su lokacin da ake samun bunkasuwar zaman al'umma. To, a gun tarurukan shekarar bana da ake yi yanzu, mene ne batutuwan da jama'a suka fi kula da su? Yanzu ga wani bayanin musamman da wakilanmu suka aiko mana.

"Muna mai da hankali kan tarurukan nan 2. Maganganun da muke kulawa suna da yawa. Alal misali, mun fi kulawa da maganar yawan kudaden karatu da makarantu suke karba da kudaden likitanci da maganar yadda za a raya biranen da muke zaune da dai sauransu."

Wannan mutumin da yake ba da amsa ga wakilinmu shi ne Xu Zhengpeng, wani dan birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lokacin da ingancin zamantakewar jama'ar kasar Sin yake samun kyautatuwa, suna kuma mai da hankula sosai kan muhimman al'amuran siyasa da na tattalin arzikin kasar.

A gun taruruka 2 na shekarar bana, wakilan majalisar dokokin kasar da membobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar za su tattauna shirin tsari na 11 na shekara-shekaru 5 don bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin. Mr. Han Meng, wani shehun malami ne na sashen ilmin tattalin arziki na jami'ar yin nazari kan ilmomin zaman al'umma ta kasar Sin, ya bayyana cewa, abin da ya fi kulawa shi ne wannan tsari.

"Na fi kulawa da abubuwan wannan tsari da za a gabatar a filla filla tare da sabuwar hanyar neman bunkasuwar tattalin arziki. Sannan kuma na fi kulawa da yadda za a kyautata tsarin tattalin arziki da raya tattalin arziki kuma da dokokin da za a tsara domin tabbatar da cimma tsarin da ake tsara."

Bugu da kari kuma, a gun taruruka na shekarar bana, an fi mai da hankali kan maganganun da suke shafar aikin gona da manoma da harkokin kauyuka domin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta bayar da manufofin raya sabbin kauyuka a nan kasar Sin. Mr. Fu Zhikang, wani wakilin majalisar dokokin kasar Sin wanda ya zo daga lardin Sichuan, ya ce, ko za a iya raya sabbin kauyuka da kyau, dole ne a ga ko manoma su samu moriya, ko za a iya daidaita maganganun da suka fi jawo hankulan manoma. Mr. Fu ya ce, "A gun wannan taro, zan nemi majalisar gudanarwa ta kasar Sin da ta kara zuba jari a cikin ayyukan noma, musamman a kan ayyukan yau da kullum da suke shafar tuddai da ruwa da gonaki da gandun daji da hanyoyi iri iri. Sabo da haka ne za a iya kafa tushe mai karfi domin karuwar hatsi da kudaden da manoma suke samu da kyautatuwar hanyoyin raya aikin gona."

Batutuwa daban da suke jawo hankulan jama'a su ne batutuwan da ke shafar zamantakewar jama'a. Kamar misali, kudaden karatu da makarantu suke karba suna da yawa yayin da kudaden likitanci da asibitoci suke karba suna da yawa da dai makamantansu. Yanzu gwamnatin kasar Sin tana kokarin daidaita irin wadannan maganganu.

Mr. Li Wen, wani kwadago mai ritaya ne da ke da zama a birnin Lanzhou na lardin Gansu yana da wani jika namiji wanda yake karatu a wata makarantar firamare ta kauye. Tun daga yanzu, jika namiji nasa ba zai biya kudin karatu ba domin gwamnatin tsakiya ta soke kudin karatu don daliban kauyuka wadanda suke karbar ilmin tilastawa a yankunan yammacin kasar Sin. Mr. Li Wen ya ce, wannan manufa tana da kyau. Yana fatan gwamnati za ta kara mai da hankali kan zamantakewar jama'a.(Sanusi Chen)