Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-03 16:54:33    
Muhimmin aikin CPPCC shi ne ba da shawarce-shawarce kan yadda za a kafa wata zaman al'umma mai jituwa

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 3 ga watan Maris da yamma, an fara cikakken zama na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin a nan birnin Beijing. A gun bikin kaddamar da taron, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin ya bayyana cewa, muhimmin aiki da majalisar za ta yi a cikin shekarar da muke ciki shi ne, ba da shawarce-shawarce kan yadda za a aiwatar da tsari na 11 na shekaru 5 don bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin da kuma kafa wata zaman al'umma mai jituwa a kasar. Sabo da haka, za ta iya ba da sabuwar gudunmmawa kan yadda za a ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma gaba.

A gun bikin kaddamar da cikakken zama na 4 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 10, Mr. Jia Qinglin ya gabatar da wani rahoton aiki, inda da farko dai ya waiwayi aikace-aikacen da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta yi a cikin shekarar da ta gabata. Mr. Jia ya ce, "Kwamitocin musamman iri iri na majalisar da jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya na majalisar da membobin majalisar sun yi aikace-aikacen bincike sosai a kan wasu muhimman maganganu game da aikin tsara tsari na 11 na shekaru 5 don bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin. Sabo da haka, sun gabatar da ra'ayoyi masu amfani da yawa."

Jama'a masu sauraro, a nan kasar Sin, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wata hukumar koli ce da jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya daban-dabam da masu bin addinai iri iri da 'yan kabilu daban-daban suke tattaunawa kan harkokin siyasa. Membobin majalisar suna iya ba da shawarce-shawarce da ra'ayoyinsu iri iri kamar yadda ake fatan su fada. Daga karshe dai, lokacin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin take tsara manufofi, ta kan yi nazari ko daukar ra'ayoyin da membobin majalisar suka gabatar.

Lokacin da yake yin hangen nesa kan aikace-aikacen da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin za ta yi a shekara ta 2006, Jia Qinglin ya bayyana cewa, majalisar za ta ba da sabuwar gudummawa kan yadda za a aiwatar da tsari na 11 na shekaru 5 don bunkasa tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin da kafa wata zaman al'umam mai jituwa a nan kasar Sin. Mr. Jia ya ce,

"Majalisar za ta kara yin bincike sosai kan yadda za a iya kafa sabbin kauyuka na gurguzu da kasar da take kirkiro sabbin fasahohin zamani da yin tsimin yin amfani da makamashin halittu da kuma kafa wata zaman al'ummar da ke sada zumunta da yanayi, haka nan kuma za ta gabatar da ra'ayoyi da shawarce-shawarce masu amfani ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin. Sannan kuma, za ta kara mai da hankali kan matsalolin da ake gamuwa da su lokacin da ake raya zaman al'umma da zamantakewar jama'a. Bugu da kari kuma, za ta bayyana fatan alheri na jama'a, kuma za ta mai da hankali kan yadda za a kawar da wahalolin da suke wuyan jama'a."

Aikace-aikacen da Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin take yi suna shafar harkokin siyasa da fannonin tattalin arziki da na zaman al'umma da dai makamantansu. A cikin kwanaki 10 masu zuwa, membobi fiye da dubu 2 za su saurari tare da tattauna rahotannin aiki na gwamnatin tsakiya da na kotun koli ta jama'a da kwamitin bincike na koli na jama'a. Sannan kuma, za su ba da ra'ayoyi da shawarce-shawarce kan muhimman manufofin yin gyare-gyare da neman bunkasuwa da maganganun da suke jawo hankulan jama'a. A gun wani taron manema labaru da aka yi a kwanan baya, Wu Jianmin, kakakin wannan cikakken zama na majalisar ya ce, "A gun taron, membobin majalisar za su aiwatar da nauyinsu na yin shawarwari kan harkokin siyasa da sa ido kan ayyukan shimfida dimokuradiyya da tattaunawa kan aikace-aikacen gwamnati." (Sanusi Chen)