Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-03 17:10:59    
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin za ta yi hidima domin aiwatar da shiri na 11 na shekaru 5 da raya zaman al'umma mai jituwa

cri

A ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya bayyana cewa, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin za ta dauki aikin yin hidima domin aiwatar da shiri na 11 na shekaru 5 da raya zaman al'umma mai jituwa a matsayin muhimmin aikinta, kuma za ta ba da sabon taimako don sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasuwanni na kasar Sin daga duk fannoni.

Mr. Jia ya ba da rahoto kan ayyukan zaunannen kwamitin majalisar a gun taro na 4 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 10 ta jama'ar kasar Sin da aka bude a wannan rana. Inda ya bayyana cewa, majalisar za ta mai da hankali sosai wajen zaben muhimman batutuwa game da bunkasa sabbin kauyukan zaman gurguzu, da raya kasa irin ta zamani, kuma raya zaman al'umma mai yin tsimin albarkatun kasa da kyakkyawan muhalli, kuma za ta ba da shawarwari masu amfani ga kwamitin tsakiya na J.K.S. da majalisar gudanarwa. Ya kuma bayyana cewa, majalisar za ta kara nuna damuwa ga batutuwan zaman rayuwar jama'a, kuma za ta bayyana burin jama'a da koke-kokensu. (Umaru)