Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-27 16:33:58    
Likitancin gargajiya na kasar Sin yana taka muhimmiyar rawa a kauyukan kasar Sin

cri

Likitancin gargajiya na kasar Sin yana da tarihi mai tsawon shekaru fiye da dubu 5, wanda muhimmin kashi ne na al'adun gargajiya na kasar Sin, ya sami amincewar mutanen kasar Sin sosai, har zuwa yanzu yana taka muhimmiyar rawa a kasar Sin saboda hanyoyin shawo kan ciwace-ciwace iri daban daban da sakamakon jinya mai kyau a bayyane da kuma farashi mai araha.

Wakilinmu ya yi zantawa a kauyukan lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin a kwanan baya. A cikin shirinmu na yau za mu gabatar muku da halin da wadannan kauyuka suke ciki a fannin likitancin gargajiya na kasar Sin.

Lokacin da yake ziyarar karamin asibitin da ke kauyen Yutang na birnin Dujiangyan na lardin Sichuan na kasar, wakilinmu ya gano cewa, yawancin 'yan kauyen sun je karamin asibitin sun zabi likitancin gargajiya na kasar Sin. Madam Luo Ping ta yi wa wakilinmu bayani kan dalilin da ya sa hakan, ta ce: "Magungunan gargajiya na kasar Sin su kan shawo kan ciwace-ciwace iri daban daban amma ba tare da tasiri maras kyau da yawa ba, kuma suna da araha. Saboda haka 'yan garinmu muna son sha magungunan gargajiya na kasar Sin."

Yanzu an kafa sassan likitancin gargajiya na kasar Sin a cikin dukan kananan asibitoci fiye da 140 da ke kauyukan birnin Dujiangyan, shi ya sa kudaden da kowane dan birnin Dujiangyan ya kan kashe wajen kiwon laifya suna ta raguwa, kuma an sassauta babban nauyin da majiyyata suka dauka bisan wuyansu, musamman ma wadanda suke zaune a kauyuka a fannin tattalin arziki.

Mr. Yang Yong wani likita ne da ke aiki tare da sauran mutane 3 a wani kauye na Dujiangyan, wadanda suke kula da kiwon lafiyar mutanen da ke zama a kauyuka guda 3. Ya bayyana cewa, "Mutane fiye da dubu 5 da dari 5 da ke zama a wadannan kauyuka 3 sun fi son sha magungunan gargajiya na kasar Sin, yawan magungunan gargajiya na kasar Sin da aka yi amfani da su ya kai kashi 50 bisa dari, in an kwatanta da na dukan magunguna."

Saboda manoma suna maraba da likitancin gargajiya na kasar Sin sosai, shi ya sa hukumar lardin Sichuan ta kara karfin kafa sassan likitancin gargajiya na kasar Sin a cikin asibitoci na gundumomi da garuruwa da kuma kauyuka. Yanzu yawan 'yan kauyukan da aka yi musu jinya ta hanyar likitancin gargajiya na kasar Sin ya kai fiye da kashi 30 cikin dari da na dukan 'yan kauyukan da aka yi musu jinya a duk fadin lardin Sichuan.

Ban da wannan kuma hukumar lardin Sichuan ta kara karfin horar da masu ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin.

Shugaban hukumar kula da likitancin gargajiya na kasar Sin ta lardin Sichuan Mr. Yang Dianxing ya bayyana cewa, "an rage nauyin da aka danka wa manoma wajen yin jinya, saboda yin amfani da likitancin gargajiya na kasar Sin a kauyuka. A ganinmu, idan manoman da suka kamu da ciwo sun iya samun jinya cikin lokaci a kauyukan da suke zama, to, ba za a tsananta ciwace-ciwacensu ba, in ba haka ba za su biya kudi mai yawan gaske ba a lokacin da suke bakin mutuwa.

Kamar yadda ake ciki a lardin Sichuan, likitancin gargajiya na kasar Sin yana kara taka babbar rawa a larduna masu yawa a kasar Sin, musamman na a lardunan da ke tsakiya da yammacin kasar Sin, inda yawan 'yan kauyuka ya sami rinjaye.

Don kara goyon bayan raya sha'anin likitancin gargajiya na kasar Sin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta ci gaba da kara zuba kudi wajen kara kyautata manyan ayyuka da kayayyaki na asikitocin likitancin gargajiya na kasar Sin da ke gundummomin da ke fama da talauci da na kananan kabilu masu tafiyar da harkokinsu da kansu da kuma wadanda ke bakin iyakokin kasar Sin da kasashen waje na larduna 7 da ke tsakiya da yammacin kasar Sin a cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa.