Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-06 21:24:25    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(02/02-08/02)

cri
An gabatar da tsabobin kudi don tunawa da wasannin Olympic na Beijing a birnin Berlin na kasar Jamus a ran 3 ga wata, wadanda bankin jama'ar kasar Sin ya shirya kuma aka yi su da zinare da azurfa. Wadannan tsabobin kudi suna kunshe da tsabobin kudi na zinare 2 da na azurfa 4, an yi zane game da wasannin motsa jiki na gargajiya na kasar Sin a kansu.

Kungiyar wasan kankara na salo-salo ta kasar Sin ta tashi daga nan birnin Beijing a ran 6 ga wata da yamma zuwa birnin Turin na kasar Italiya don shiga wasannin Olympic na lokacin hunturu na karo na 20 da za a yi a nan daga ran 10 zuwa ran 26 ga wannan wata. An mayar da 'yan wasan kasar Sin Zhang Dan da Zhang Hao guda biyu daga cikin 'yan wasan da za su iya samun lambar zinare a cikin gasar wasan kankara salo-salo tsakanin namiji da mace a wannan gami.

Ban da wannan kuma akwai wani labari daban game da wannan muhimmin wasanni. An ce, ko da yake ba a sami sakamako mai kyau wajen sayar da tikitoci ba, amma bisa adadin kididdiga mai dumi dumi da kwamitin shiryawa wasannin Olympic na lokacin hunturu na Turin ya bayar a kwanan baya, an ce, an kyautata sayar da tikitoci sannu a hankali. Har zuwa ran 2 ga watan nan, an riga an sayar da tikitoci fiye da dubu dari 7, jimlar kudin da aka samu daga tikitoci ta kai kudin Euro miliyan 60 a yanzu, an rage kudin Euro miliyan 4 da za a iya tabbatar da makasudin karshe da aka kiyasta, wato kudin Euro miliyan 64.

An yi bikin jefa kuri'a cikin kungiya kungiya domin gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta mata ta duniya a birnin Sao Paulo na kasar Brazil a kwanan baya. An raba kungiyoyi 16 daga nahiyoyi 5 zuwa rukunnoni guda 4. Kungiyoyin kasashen Sin da Amurka da Rasha da kuma Nijeriya za su yi takara da juna. Kungiyar kasar Sin ba ta iya fito daga rukuninta cikin sauki ba, saboda sauran kungiyoyi 3 suna da karfi sosai. za a yi wannan gasa a kasar Brazil a watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta fara aikin horo na tsawon makanni 3 a birnin Kunming da ke kudu maso yammacin kasar Sin a ran 3 ga wata. Wannan ne karo na farko da kungiyar kasar kasar Sin ta yi horo a tudu bayan shekarar 1996. Kungiyar kasar Sin za ta yi horo har zuwa ran 22 ga watan Fabrairu, daga baya za ta tashi zuwa kasar Holland don ci gaba da horo na tsawon makonni 3, daga baya za ta je kasar Portugal, inda za ta shiga gasar cin kofin Algarve ta wasan kwallon kafa ta mata ta duniya da aka saba shiryawa sau daya a ko wace shekara.

A 'yan kwanakin nan da suka wuce, kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2006 ya sanar da cewa, bayan da aka kyautata, jimlar tikitocin gasar cin kofin duniya za ta karu kadan, jimlar tikitoci za ta kai miliyan 3 da dubu 70 gaba daya, wadda za ta karu da guda dubu 140, in an kwatanta da jimlar da aka kiyasta a da. Ko da yake haka ne, tikitocin da ake sayarwa ba su biyan bukatun mutane. Yanzu yawan tikitocin da masu son wasan kwallon kafa daga wurare daban daban na duniya suke son saya ya ninka yawan tikitocin da ake sayarwa sau 20.(Tasallah)