Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-31 17:26:01    
A yi yawon shakatawa a kasar Sin a lokacin babbar sallar garagajiya ta al'ummar Sin

cri
Ran 29 ga watan Janairu na shekarar nan ranar babbar sallar gargajiya ce ga al'ummar Sin wato Spring Festival a Turance. Wannan babbar sallar gargajiya ta al'ummar Sin ta tashi daidai da babbar salla ga musulmi.

A kan shirya gagaruman bukukuwa a lambunan shan iska da dakunan Ibada a lokacin babbar sallar gargajiya ta al'ummar Sin. Yau da shekaru darurruwa ke nan da aka shirya irin wadannan bukukuwa a nan Beijing, babban birnin kasar Sin. A lokacin bukukuwan nan, a kan kayatar da lambunan shan iska, mutane masu dimbin yawa kan runtuma zuwa lambunan don kallon wasannin raye-raye da aka yi cikin shiga burutun zakoki da na dodanni da sauransu, sun ci kayan abinci irin na gargajiya na birnin Beijing, su sayi filafilai da mutum-mutumin da aka yi da yumbu da sauran kayayyakin fasaha iri daban daban. Haka zalika shekarar nan shekarar kare ce bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Sabo da haka za a shirya nune-nunen shahararrun karnuka, a gabatar da wasanni a kan yadda ake horar da karnuka da makamantansu a gun bukukuwan nan.

Malam Zhang Shuo, wani manajan babban kamfanin yawon shakatawa na kasa da kasa na Sin ya bayyana cewa, "yayin da kamfaninmu ya karbi masu yawon shakatawa da suka zo birnin Beijing a lokacin babbar sallar gargajiya ta al'ummar Sin, mu kan kai su zuwa irin wadannan bukukuwa da ake yi a lambunan shan iska da dakunan Ibada, inda masu yawon shakatawa za su ganam ma idanunsu game da tsabi'ar musamman ta birnin Bejing. Tun da yake shekarar nan shekarar kare ce bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, to, ba makawa, duk bukukuwan nan za su gwada irin al'adun gargajiya na kasar Sin a kai."

A kan shirya gaggaruman bukukuwan nan musamman a wurare uku a birnin Beijing wadanda suka hada da dakin ibada na addinin Tao da ake kira Baiyunguan cikin Sinanci, da dakin ibada mai suna Dongyue da kuma dakin Ibada mai suna Ditan inda sarakunan kasar Sin na zamanin da suke bauta wa Allah a duniya.

Malam Li Weihua, jami'in kwamitin shirya bukukuwan babbar sallar gargajiya ta jama'ar Sin a nan birnin Beijing ya ce, "masu yawon shakatawa wadanda suka fito daga Amurka da Japan da Korea ta Kudu da kasashen Turai da kuma wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya su kan halarci bukukuwan nan don ganam ma idanunsu abubuwa masu ban sha'awa na babbar sallar gargajiya ta jama'ar Sin."

Bayan birnin Beijing, sai mu zagaya birnin Nanjing wanda shahararren tsohon babban birnin kasar Sin ne a lokacin daulolin gargajiya guda 10 na zamanin da. A halin yanzu birnin Nanjing fadar gwamnatin lardin Jiangsu ne na kasar Sin. A nan, a kan shirya bikin nune-nunen fitilun gargajiya masu kyaun gani iri daban daban a dakin ibada na Confucius na birnin tun daga ran 1 zuwa ran 18 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Yawan masu yawon shakatawa wadanda su kan je wannan dakin ibada don more idonsu da wadannan fitulu masu ban sha'awa ya kan kai dubu darurruka. Da Malam Yang Ming, manemi labaru na lardin Jiangsu ya taba magana a kan bikin, sai ya ce, "yawan fitilu da za a nuna a dakin ibada na Confucius na birnin Nanjing a lokacin babbar sallar gargajiya ta jama'ar Sin zai kai dubu 450 har ba a taba ganin irin yawan nan ba a da. Makasudin shirya wannan gaggarumin nunin fitilun gargajiyar Sin shi ne domin gwada irin kyakkyawan hali mai armashi da ake ciki a birnin Nanjing. "

Daga birnin Nanjing, sai mu leka birnin Guangzhou da ke a kudancin kasar Sin. A kan shirya bikin nunin kyawawan furanni a birnin Guangzhou a lokacin babbar sallar nan. Ya zuwa yanzu, an yi ta shirya irin wannan bikin nunin furanni ne a ko wace shekarar har cikin sama da shekaru 200 da suka wuce.

Idan masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje sun sami damar zuwa birnin Guangzhou a lokacin babbar sallar gargajiya ta jama'ar Sin, to, ba makawa ya ziyarci bikin nan don jin dadi da more idanunsu da wadannan kyawawan furanni iri daban daban. (Halilu)