
Mr. Shigeru Omi ya jaddada cewa, lokacin da ake yi wa tsuntsayen gida allurar rigakafi, a sa'i daya kuma, ya kamata a kyautata halin da ake ciki wajen shawo kan cututtuka tsakanin tsuntsayen gida da kuma kiwonsu, da kuma daga matsayin kiwon tsuntsayen gida da shawo kan cututtuka masu yaduwa ta hanyar kimiyya.
Ko da yake ba a sha samun annobar murar tsuntsaye a wannan mako ba, in an kwatanta da watannin da suka gabata, amma ba za a iya ganin cewa, barazanar irin wannan annoba ta riga ta bata ba. Mr. Shigeru Omi ya tuna wa mutane cewa, wannan mummunar annoba ta kan bullo a lokacin hunturu, mai yiwuwa ne za a sake samunta a lokacin hunturu na shekarar da muke ciki da kuma lokacin bazara na shekara mai zuwa, saboda haka, kada a yi sako-sako da lamarin. Ya kuma yi bayani cewa, kungiyar WHO ta riga ta ba da shawara ga ma'aikatan kiwon lafiya da aikin noma na kasar Sin da su kara horar da ma'aikatan shawo kan cututtukan da suke aiki a kauyuka, wadanda za su taka rawa a farko-farkon lokacin gano cutar da kai rahoto da kuma shawo kan cututtukan.(Tasallah) 1 2 3
|