Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-14 11:08:16    
Lebanon ta nemi a kafa kotun musamman na kasashen duniya domin yanke hukunci kan matsalar Halili

cri
A ran 13 ga wata, Ibrahim Assaf, wakilin dindindin na kasar Lebanon da ke M.D.D. ya bayyana cewa, Lebanon tana fatan kafa wata kotun musamman na kasashen duniya domin yanke hukunci kan dukkan matsaloli ciki har da Halili, tsohon firayim ministan Lebanon wanda aka yi masa kisan gilla.

Mr. Assaf ya yi wannan bayani ne bayan da ya saurari rahoton da Detlev Mehlis, shugaban kwamitin kasashen duniya na yin bincien matsalar Halili ya yi a wannan rana a kwamitin sulhu na M.D.D.

Mr. Assafa ya ce, idan ana son tabbatar da zama mai karko da kwanciyar hankali na shiyya-shiyya, dole ne a yi binciken dukkan matsalolin kisan gilla da aka yi daga shekarar 2004 zuwa yanzu sosai, kuma yanke wa masu laifi hukunci yadda ya kamata, ciki har da kisan gillar da aka yi wa Halili da Gibran Tueni a kwanan baya. (Umaru)