Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-02 18:19:30    
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin

cri

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wata hukuma ce mai muhimmanci da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ke ja ragamarta don yin hadin guiwar tsakanin jam'iyyun siyasa da yawa da ba da shawara kan harkokin siyasa.

Kasar Sin wata kasa ce mai yawan mutane da kabilu da kuma jam'iyyun siyasa. Sabo da haka kafin kasar Sin ta tsai da manyan manufofi, wajibi ne, ta yi shawarwari sosai a tsakaninta da mutanen bangarori dabam daban don kara karfin hadin guiwar tsakanin kabilu dabam daban da jam'iyyu da bangarori da kuma mutane da ba na cikin ko wace jam'iyya ba, ta yadda za a kara bunkasa harkokin raya zaman gurguzu. Tun da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, majalisar ta kan yi tattaunawa sosai ga batun bunkasa harkokin tattalin arziki, da na siyasa da zamantakewar al'umma da sauran manyan batutuwa. Ta hanyar nan ce, manufofi da dokoki da ake tsara za su dace da burin yawancin mutanen kasar Sin da kuma moriyarsu.

An shirya cikakken zaman taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin a birnin Beijing tsakanin ran 21 zuwa ran 30 ga watan Satumba na shekarar 1949. Wakilai 662 sun hallarci wannan taron, inda aka zartas da tsarin ka'idoji na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin wato tsarin mulki na wucin gadi na kasar Sin. A gun wannan taro an zabi Mao Zedong don ya zama shugaban gwamnatin tsakiya ta Jamhuriyar Jama'ar Sin, an kuma zabi Mr. Zhu De da Mr. Liu Shaoji da madan Song Qinglin da sauran mutane uku don su zama mataimakansa. Haka nan kuma an yanke shawara cewa, jar tuta mai rawayen taurari biyar ta zama tutar Jamhuriyar Jama'ar Sin, wakar mai suna " macin sojojin sa kai " ta zama taken kasa, an mayar da birnin Beijing da ya zama hedkwatar kasa, haka nan kuma an mayar da ran 1 ga wata Oktoba don ta zama ranar bikin kasa.

A karkashin tsarin ka'idojinta na yanzu, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ta kafa kwamitin duk kasa da zaunannen kwamiti da kwamitocin musamman guda 9 bisa matakin tsakiya, haka kuma ta kafa kwamitocinta a wurare dabam daban bisa matakin wuri-wuri. Wa'adin aikin ko wace majalisar na shekaru biyar biyar ne, kuma a kan shirya cikakken zaman taron majalisar a ko wace shekara.

Ma'amallar da ake yi tsakanin majalisar da kasashen waje wani babban kashi ne ga harkokin waje da kasar Sin ke yi. A tsakanin shekarar 1998 zawu ta 2003, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin ta aika da kungiyoyinta 88 zuwa kasashe 76 don yin ziyara, yayin da ta karbi kungiyoyi 69 da suka zo daga kasashe 34 don yin ziyara a kasar Sin. Ya zuwa yanzu, majalisar ta kulla huldar aminci a tsakaninta da hukumomi 158 na kasashe 95 da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya guda 6.